A zamanta na yammacin jiya ne kotun ta bayyana matsayinta dangane da karar da kungiyoyin fafatuka suka shigar a gabanta na bukatar ta dakatar da matakin hanin da Magajin gari ya dauka ta kuma basu damar fita tituna a jiyan kamar yadda suka kudurta a ci gaba da kalubalantar gwamnatin Jamhuriyar Nijar.
Kungiyoyin sun bayyana cewa, suna masu biyayya ga hukumcin kotun, amma zasu dakaka kara zuwa kotu ta gaba.
Kakakin kungiyar Suraju Isa ya bayyana cewa, qa matsayinsu na kungiyoyi masu biyayya da doka, sun yarda da abinda alkaki ya fadi amma wannan ba zai hanasu ci gaba da fafatuka ba. Ya jadada cewa zasu daukaka kara a babban kotu
Yace matakan da hukumomi ke dauka sun tabbatar da korafe korafen da suke yi cewa, damokaradiya ta shiga wani irin hali a Jamhuriyar Nijar. Yace wadannan matakan da ake dauka basu cikin kundin tsarin mulkin kasar.
Kungiyoyin dai sun shiga wannan fafatuka ne da nufin neman gwamnati ta dauki mataki a fannonin ilimi, kowon lafiya, zamantakewa da dai sauransu da suka ce sun jefa al’ummar Jamhuriyar Nijar cikin halin kunci.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Sule Mummuni Barma ya aiko mana daga birnin Nyamie.