Tarukan biyu sun samu mahalarta daga kasashen biyu saboda samun zaman lafiya mai dorewa tsakanin Fulani makiyaya da manoman kasashen biyu.
Tarukan sun zama wajibi domin makiyaya su kan tsallaka iyakokin kasashen. Fulanin Nijar na shiga Najeriya haka ma na Najeriya na shiga kasar ta Nijar banda kasuwannin dabbobi dake tsakaninsu.
Malam Ahmadu Halilu shugaban kungiyar Fulanin Nijar yace sun kira kungiyoyin manoma da makiyaya domin su yi nazari akan hanyoyin da zasu zauna lafiya. Yace kowace sana'a na bukatar zaman lafiya. Yadda mutane suke da hanyoyin bi haka ma yakamata a kebewa dabbobi hanyoyin da zasu bi.
A nasa bangaren Malam Ali Muhazari shugaban fulani daga tarayyar Najeriya yace tarukan zasu bada damar yadda za'a shimfida zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a kasashen biyu.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani