Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Sauya Ranar Sauraron Shari’ar Nnamdi Kanu Zuwa Ranar 18 Ga Watan Janairu Mai Zuwa.


Nnamdi Kanu da lauyoyinsa a zaman kotun da aka yi a ranar Alhams (Channels TV)
Nnamdi Kanu da lauyoyinsa a zaman kotun da aka yi a ranar Alhams (Channels TV)

Mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta gabatar da shari’ar da ake yi wa shugaban kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biyafra, Nnamdi Kanu, inda ta sauya ranar shari’ar daga ranar 19 zuwa 18 ga watan Janairun shekarar 2022.

Sauya ranar shari’ar ya biyo bayan rage wa’adin da alkali ya yi ne bayan da ya sigar da bukatar neman sauya ranar da kotu ta tsaida a baya.

Lauyan Nnamdi Kanu wato, Ifeanyi Ejiofor ya shigar da bukatar hakan ne a gaban kotun da ta amince da yin shari’ar a tsakanin watan Nuwamba da Disamban shekarar nan ta 2021 sabanin ranar 19 ga watan Janairun shekarar 2022.

Lauyan Nnamdi Kanu, Ifeanyin Ejiofor.
Lauyan Nnamdi Kanu, Ifeanyin Ejiofor.

A nasa bangaren, lauyan gwamnatin tarayya, Shuaib Labaran, ya shaida wa kotun cewa, gwamnatin kasar ta cika wata takardar affidavit da ta bukaci a yi watsi da bukatar Nnamdi Kanu din.

Sai dai mai shari’a Binta Nyako a yayin gabatar da shari’ar ta sanarda lauyan Kanu cewa ba za a yi la’akari da bukatarsa ta ci gaba da yin shari’ar a lokacin da ya bayyana ba saboda babu lokacin a shari’ance a kan irin wannan batu.

Tawagar lauyan Nnamdi Kanu.
Tawagar lauyan Nnamdi Kanu.


Biyo bayan hakan ne mai shari’a Nyako ta dage shari’ar ta amince da sauya wasu shari’o’in da aka shirya yi a ranar 18 ga watan Janairu domin sauraron na Kanu da su matakin dage shari’un na ranar 18 din da za a yi har zuwa ranar 19 da 20 ga watan Janairu.

Mai shari’a Nyako ta kuma umurci hukumar tsaron farin kaya wato DSS da ta bai wa Kanu damar ci gaba da yin addininsa a tsare, ya canza tufafinsa, sannan ya sami kwanciyar hankali a wurin da ake tsare da shi.

Kotu ta bayar da wannan umarni ne a yayin da Nnamdi Kanu bai halarci zaman cikin kotun ba.

Haka kuma, sabanin yadda aka saba gani idan za a yi zaman kotu kan shari’ar Nnamdi Kanu ana jibge jami’an tsaro a hanyoyin da ke kusa da babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau ba bu alamar hakan ko kadan inda ba a ga yawan mutane a cikin kotu ba, kamar ba shari’ar shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ba.

Harabar babbar kotun taryyar Abuja.
Harabar babbar kotun taryyar Abuja.

Daga daren ranar Talata ne aka fara rade-radin cewa Nnamdi Kanu zai bayyana a gaban kotu a yau, sabanin ranar 19 ga watan Junairu shekarar 2022 da aka dage zaman shari’arsa zuwa cikin watan Nuwamba.

Idan ana iya tunawa, tun bayan kama madugun kungiyar IPOB Nnamdi Kanu aka dawo da shi Najeriya an yi zaman sauraron shari'arsa a watannin Yuli, Oktoba da ma Watan disamban nan da mu ke ciki a bisa zargin cin amanar kasar, harzuka magoya bayansa su dauki makami da dai sauransu.

XS
SM
MD
LG