Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Ohanaeze Ta Yi Karin Haske Kan Kafa Kwamitin Bin Diddigin Shari'ar Nnamdi Kanu


Cif Alex Ogbonnia.
Cif Alex Ogbonnia.

Kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, ta yi karin haske game da kwamitin lauyoyin da ta kafa, don bin diddigi da kuma sa ido a shari'ar da ake yi wa Mazi Nnamdi Kanu, madugun kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, yayin da zai ci gaba da gurfana a gaban kotu.

A wata hira da Muryar Amurka yau, kakakin kungiyar Ohanaeze, Cif Alex Ogbonnia, ya fadi cewa, alhaki ya rataya ne akan kungiyar Ohanaeze Ndigbo, ta kare hakkin duk wani dan kabilar Igbo, idan akwai bukata ta yi hakan, in da ya kara da cewa:

"Mun dauki kafa wannan kwamitin da muhimmanci. Bama shakkan tsarin shari'armu. Amma abin da muke cewa anan shine Nnamdi Kanu dan mu ne. Nnamdi Kanu dan kabilar Igbo ne, kuma kowane dan kabilar Igbo danmu ne. Shi yasa muka kafa wannan kwamiti na masanan shari'a, don mu san abin da ke faruwa a kotu, da kuma yadda tsarin ke tafiya."

Dakta Hagler Okorie, wani lauya da kuma malamin jami'a, yayi tsokaci game da kafa shi wannan kwamitin. Ya ce, "Sun yi haka ne a matsayin kungiya mai zaman kanta, kuma kungiya mai zaman kanta tana iya cewa tana so ta sa ido a wannan shari'ar, domin tabbatar da adalci. Kwatakwata wannan ba wata matsala ba ce, kuma a nawa tunanin, membobin wannan kwamitin zasu kasance ne a kotu mai yiwuwa a matsayin abokanen kotu, su bi diddigin shari'ar, ba wai zasu yi wa shari'ar wani shisshigi ba. Wannan batun fa kai tsaye ya ke sosai, kuma ya shafi abin da dokar Najeriya ta tanadar. Na farko dai ya tsallake beli ya ware na tsawon shekaru. Wannan shi ake dubawa, da kuma sauran laifuka da ake tuhumarsa da su."

Wannan shine karo na farko, da kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ke yin wani furuci, tun da gwamnatin Najeriya ta kado Mazi Nnamdi gida.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

XS
SM
MD
LG