Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Najeriya Ta Jinkirta Hukunci Kan Karar Da Jihohi Ke Kalubalantar Dokar Shugaban Kasa Ta 10


ABUJA: Taron alkalai

Dokar ta tilastawa dukkan jihohi da su hada da kason kudaden bangaren shari’a da na majalisun dokoki a cikin kasafin kudinsu.

Kotun Kolin Najeriya ta jinkirta ba da hukunci kan karar da jihohi 36 na kasar suka shigar a gabanta inda suke kalubalantar sahihancin dokar shugaban kasa ta 10 ta shekarar 2020.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ne ya kafa dokar ta 10, tare da rattaba mata hannu a ranar 22 ga watan Mayun shekarar da ta gabata ta 2020.

Dokar ta tilastawa dukkan jihohi da su hada da kason kudaden bangaren shari’a da na majalisun dokoki a cikin kasafin kudinsu.

To sai dai a yayin da suka nuna rashin gamsuwa da dokar, gwamnatocin jihohin ta hanyar kwamishinoninsu na shari’a, sun shigar da kara mai lamba SC/655/2020 inda suke kalubalantar dokar.

Jihohin na neman kotun ta fayyace ko matakin shugaban kasa na yin dokar da ta tilastawa jihohi samar da kudade ga kotunan jihohi ya sabawa sassa na 6, 80, 81, 120 da kuma 121 na kundin tsarin mulki, da ya dora alhakin samar musu da kudade akan gwamnatin tarayya.

A zaman kotun dai, lauya mai wakiltar jihohin masu kara, Augustine Alegeh (SAN), ya ce bai kamata albashi da wasu alawus-alawus na alkalai su kasance a cikin kowane kasafin kudi ba.

Ya kara da cewa sashe na 84(4) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ya yi tanadin cewa ana samun wadannan kudaden ne daga cikin kudaden shiga da ake tarawa, ba wai a cikin kasafin kudi ba.

To sai dai kuma bayan sauraren wakilan duka bangarorin da ke cikin shari’ar, kotun kolin mai alkalai 7, a karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dattijo, ta jinkirta ba da hukunci a kai.

Tun lokacin da aka kafa dokar ta shugaban kasa ta 10 a shekarar bara, ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, wadanda suka lashi takobin ganin bayan dokar.

Gwamnatin tarayya dai ta ce dokar ta shugaban kasa ta 10 ta zo ne a daidai lokacin da ake ta kiraye-kirayen samar da ‘yancin cin gashin kai ga bangarori 3, da suka hada na shari’a da majalisun dokoki da kuma na kanana hukumomi.

Gwamnatin tarayyar wadda a can baya ta zargi gwamnonin jihohi da yin kafar angulu wajen tabbatar da ‘yancin cin gashin kan wadannan bangarorin, ta ce dokar na da manufar ganin an aiwatar da ‘yancin sarrafa kudaden wadannan bangarorin, tare da cire su a karkashin ikon gwamnoni da ke amfani da wannan damar suna juya su yadda suke so.

To sai dai kuma a nasu bangare, gwamnatocin jihohin suna ganin babu wata hujja da gwamnatin tarayya za ta tilasta musu nauyin da doka ta dora mata, ko kuma yi musu shisshigi da katsalandan a tsarin tafiyar da jihohinsu.

XS
SM
MD
LG