Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al-Shabab ta Dauki Alhakin Harin da Aka Kai a Mogadishu


Wannan dai shine karo na biyu da kungiyar ta auna fadar wata gundumar dake cikin babban birnin na Magadishu a cikin wannan watan.

Mahukunta a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, sun ce wata mota da aka saka bam a cikinta tayi bindiga a fadar wata gunduma dake birnin kuma tayi musabbabin mutuwar mutane 6 kana wasu mutane 16 sun samu rauni.

Shi dai wannan harin ya auna fadar gundumar Hodan ne dake Mogadishun. Shedun gani da ido sun ce wannan harin motar na yau Litinin yayi mummunar illa ga ginin ko baya ga kashe mutane.

Wani jami’in ‘yan sanda mai suna Ibrahim Mohammed ya shaidawa kanfanin dillacin labarai na AFP cewa wannan fashewar bomb din mai muni ce sosai.

Tuni dai kungiyar Alshabab ta dauki alhakin kai wannan harin.

Missali a ranar 2 ga wannan watan wani harin bam irin wannan na mota da ‘yan kunar bakin wake suka kai ya tatarwatsa hedikwatan gundumar Hawlwadag inda mutane 3 suka mutu.

Facebook Forum

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG