Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar IPOB Ta Yi Kira Ga Buhari Ya Saki Kanu Kafin 29 Ga Mayu


Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu

Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo, Cif Emmanuel Iwuanyanwu ya sake rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saki Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB.

Iwuanyanwu ya ce ‘yan kabilar Igbo ba zasu balle daga Najeriya ba saboda suna ko'ina kuma ba zasu bar jarinsu ba.

A cewar jaridar Daily Post, shugaban na IPOB ya yi wannan roko ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a wurin aikin yashe tafkin Oguta – Kogin Orashi a jihar Imo.

Nnamdi Kanu, a tsakiyar wasu lauyoyi a kotu
Nnamdi Kanu, a tsakiyar wasu lauyoyi a kotu

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yami Osinbajo ne ya wakilci shugaban kasa Buhari a wurin taron.

Iwuanyanwu ya ce ya kamata Buhari ya saki Nnamdi Kanu kafin ya bar ofis a tanar 29 ga watan Mayu.

Ya ce, “Mataimakin shugaban kasa, ka gaya wa dan uwanmu, dan mu Buhari cewa Ohaneze Ndigbo da ke da mutane sama da miliyan 60 ta bukaci ya saki Nnamdi Kanu. Igbo ba su ballewa. Ban ga dalilin da zai sa wani zai ce Igbo na ballewa ba. Igbo suna ko'ina. Muna da jari, za mu bar jarinmu?

Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu

“Don haka don Allah ina mika masa wannan sakon ne saboda shi ne shugabana a Najeriya amma a Ohaneze Ndigbo, mu mun karrama shi kuma mamba ne.

Don haka ni ne shugabansa a can. To yanzu ina gaya masa cewa a saki Nnamdi Kanu kafin ya tafi. Za mu yi godiya sosai."

XS
SM
MD
LG