Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Fitar Da Hotan Bidiyon Mutanen Da Suka Kai Hari Faransa


Kungiyar nan mai da'awar jahadi ISIS, ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna mutane biyun nan da su ka kashe wani Limamin Katolika, a wata Majami'a a arewa maso gabashin Faransa, su na dauke da wani kwali mai sakon ISIS, su na shelanta mubaya'arsu ga Shugaban ISIS Abu Bakr al-Baghdadi.

Wani kamfanin yada labarai mai alaka da ISIS ne ya yada faifan bidiyon. A cikin faifan bidiyon, daya daga cikin maharan na karanta mubaya'arsu ga al-Baghdadi da harshen Larabci kamar yadda al'adar ta ke.

Tun da farko jiya Larabar, Shugaban Faransa Francois Hollande ya gana da Shugabannin addinai a wani yinkuri na kawar masu da tsoro bayan hare-hare na baya-bayan nan a Faransa.

Hollande ya tara Shugabannin addinai daban-daban a ofis dinsa a birnin Paris, a wani mataki na tabbatar da hadin kan addinan.

Har yanzu da dama daga cikin 'yan Katolika na kasar ta Faransa na cikin kaduwa bayan harin na ranar Talata da wani yaro dan shekaru 19 da haihuwa, wanda dama ana tuhumarsa kan wasu ayyukan ta'addancin, ya kai ta wajen kutsawa cikin wata Majami'a tare da wani, su ka yanka Limamin Majami'ar a daidai lokacin da ya ke gudanar hidimar addini ta Mass.

Sau biyu ake kama Adel Kermiche bisa zargin aikata ta'addanci tun a watan Maris na 2015, kuma ya na dauke da na'urar nuna inda mutum ya ke a lokacin da ya kai harin na karshe.

XS
SM
MD
LG