Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISWAP Ta Yi Garkuwa Da Mutane Uku a Jihar Borno


Motar kungiyar ISWAP a garin Baga na jihar Borno.
Motar kungiyar ISWAP a garin Baga na jihar Borno.

Mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ke fama da tashe-tashen hankula, sun yi awon gaba da wani ma'aikacin agajin jin kai da wasu jami'an yanki biyu, a cewar jami’an tsaro a ranar Laraba.

Mayakan ‘yan ta’adda na kungiyar ISWAP ne suka yi garkuwar da mutanen a wani shingen binciken ababen hawa a kauyen Wakilti, da ke jihar Borno a ranar Litinin, kamar yadda majiyar ta shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP, a wani lamari na baya-bayan nan da ya faru a yankin da ke fama da rikicin ‘yan ta’adda sama da shekaru goma.

"Wadanda aka yi garkuwar da su sun hada da jami'an yankin guda biyu da kuma wani ma'aikacin agaji, amma ba a bayyana kungiyar da yake aiki ba," in ji daya daga cikin majiyoyin tsaron.

Jami’an biyu suna kan hanyarsu ne ta komawa Maiduguri babban birnin yankin daga garin Mobbar, inda suka je zaben kananan hukumomi da aka gudanar a karshen mako, majiya ta biyu ta ce.

A watan Yunin da ya gabata an kashe ma’aikatan jinkai biyar ‘yan kwanaki bayan sace su da kungiyar ‘yan ta’addar ISWAP ta yi, wacce ke da karfi a yankin Tafkin Chadi.

Zaben na kananan hukumomi a jihar Borno, shi ne na farko da aka gudanar tun bayan da kungiyar Boko Haram ta fara tayar da kayar baya a shekarar 2009.

XS
SM
MD
LG