Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Izala Tayi Taron Horaswa Kan Sabbin Dabarun Bada Agaji


Musulman Najeriya

A kokarinta na karfafa da inganta aikin agaji a ciki da wajen Najeriya kungiyar Izala ta shirya taron horas da mutane kan sabbin dabarun aikin agaji.

Kungiyar Izala ta shirya taron horas da 'yan agaji wadanda zasu yi aiki a cikin Najeriya da ma wasu kasashen duniya.

'Yan aikin agajin da kungiyar izala ke horaswa basu da albashi kuma basa daukan makamai. 'Yan agajin suna aiki a Najeriya da kasashen yammacin Afirka har ma zuwa Saudiya. Daya daga cikin kwamandojin 'yan agajin Uztaz Salisu Mohammed Gombe ya ce aikin 'yan agajin na sa kai ne kuma sukan taimaki duk mai bukatan taimako. Ya ce duk abun da kungiyar ta mallaka na duk wadanda suka yi kalmar shahada ne, wato na duk kowane Musulmi ne.

Dabi'un 'yan agajin sun birge Hassan Dankwanbo gwamnan jihar Gombe inda ya ce sun cancanci samun tallafin gwamnati a kowane matakai. Ya ce idan so samu ne kowane matashi ya kamata ya yi irin horaswar. Ya yiwa kungiyar murna da jinjina mata. A wasu kasashe har da Amurka kafin mutum ya kai wani mataki dole sai ya yi aikin taimakawa jama'a. Kafin mutum ya zama gwamna sai yi irin aikin da suke yi. Ya ce kafin mutum ya zama shugaban kasa sai ya yi aikin jinkai domin bata yiwuwa mutum da bai san hakin dan adam ba ya yi masa shugabanci.

Daya daga cikin masu wa'azi a wurin horaswar Sheikh Nasiru Abdulmuhuyi ya ce irin amanar 'yan agajin ake bukata wurin yakar cin hanci da rashawa a Najeriya. Ya ce a cikin dare suke zuwa neman taimako, kuma a cikin dare ake kawo kudaden da aka tara kuma taro ba zai salwanta ba.

'Yan agajin na samun horaswa kowace shekara domin aikinsu ya tafi daidai da na zamani ta hanyar inganta tsaro a filayen wa'azi da masallatai da kuma lokacin taron wa'azi na kasa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG