Accessibility links

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kawuri Cikin Jihar Borno Suka Kashe Fiyeda Mutane 40


'Yansanda a jihar Barno suke gadi wata babbar mota da ake zargin 'yan Boko Haram suka kona.

'Yan binidga sun kashe fiyeda mutane 40 a kawuri dake karamar hukumar kwanduga cikin jihar Barno.

Jami'an tsaro sun tabbatar da rahotannin harin da wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai kan kauyen kawuri dake cikin karamar hukumar kwanduga a jihar Borno.

Lamarin ya auku ne jiya lahadi sa'ilinda kasuwar kauyen take cike makil ana hada hadada.

Kwamishinan 'Yansandan jihar Borno Tanko Lawal wanda ya tabbatar da wannan labari ga wakilin Sashen Hausa dake yankin, yace maharan sun kona fiyeda rabin garin, suka raunata mutane fiyeda ashirin.

Mazauna kauyen sun shaidawa wakilinmu cewa yawan wadanda 'yan bindigan suka halaka ya haura hamsin.

Ahalin yanzu da yawa daga cikin mutanen kauyen sun fara gudu daga kauyuka dake yankin zuwa manyan alkariyu, ko su tsallaka zuwa kasashe dake makwabtaka da Najeriya.

XS
SM
MD
LG