Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama Ta Ce 'Yan Awaren Kamaru Suna Kai Hari Kan Makarantu


Makaranta A Kamaru

Wata kungiyar kare hakkin bil'adama wato Human Rights Watch ta kasa da kasa yau Alhanis, ta zargi mayakan 'yan awaren yankin Anglophone na kasar Kamaru dakaiwa makarantu da dalibai da malamai hari a lokacin yakin basasa da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Hare-haren sun tilastawa biyu daga cikin ukun makarantu na yankunan masu magana da Ingilishi na Kamaru rufewa, tare da hana dalibai sama da 700,000 samun ilimi, in ji kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch (HRW) da ke Amurka a cikin wani rahoto.

Rahoton ya bayyana hare-haren da aka kai a kalla makarantu 70 tun daga shekarar 2017, lokacin da gwamnatin kasar ta murkushe masu zanga-zangar lumana, ya haifar da kazamin rikici tsakanin sojojin gwamnatin da galibin masu amfani da harshen Faransanci da kuma masu amfani da turancin Ingilishi.

'Yan awaren da ke son kafa kasar ballewa mai suna Ambazonia, sun bukaci makarantun da ke kusa da su yi zanga-zangar nuna adawa da tsarin karatun gwamnati - kuma sun kai hari kan wadanda ba su bi ba.

Rahoton ya ce sun kashe tare da sace daruruwan dalibai da malamai, sun lalata makarantu, da yi wa iyaye barazana, suna masu cewa dole ne su ajiye su a gida, kuma sun yi amfani da makarantu a matsayin sansanin garkuwa da azabtarwa.

Ilaria Allegrozzi, marubuciyar rahoton ta rubuta "Wadannan hare-haren masu laifi ba kawai suna haifar da lahani na zahiri da tunani ga wadanda abin ya shafa ba; suna jefa rayuwar dubun dubatar dalibai cikin hadari."

Kamfanin dillancin labarai na Reutersbai samu jin ta bakin shugabannin ‘yan awaren ba nan da nan a lokacin da ya tuntube su.

XS
SM
MD
LG