Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samuel Eto'o Ya Zama Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Kamaru


Samuel Eto'o

Hakan na nufin Eto'o, wanda ya lashe lambar gwarzon dan kwallon Afirka har sau 4, zai jagoranci hukumar kwallon kasar ta kamaru na tsawon wa’adin shekaru 4.

Tsohon shahararren dan wasan kasar Kamaru Samuel Eto'o, ya lashe zaben shugabancin hukumar kwallon kafar kasar ta Kamaru da aka gudanar a yau Assabar.

Eto'o ya lashe zaben ne da kuri’u 43, inda ya kada babban abokin takararsa, Seydou Mbombouo, wanda yanzu haka yake kan karagar shugabancin hukumar, haka kuma shi ne mataimakin shugaba na 4 na hukumar kwallon kafar nahiyar Afirka wato CAF, wanda ya sami kuri’u 31.

Samuel Eto'o ya lashe zaben shugabancin hukumar kwallon Kamaru
Samuel Eto'o ya lashe zaben shugabancin hukumar kwallon Kamaru

Hakan na nufin Eto'o, wanda ya lashe lambar gwarzon dan kwallon Afirka har sau 4, zai jagoranci hukumar kwallon kasar ta kamaru na tsawon wa’adin shekaru 4, inda zai karbi mulkin hukumar a daidai lokacin da kasar za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka a watannin Janairu da Fabrairu masu zuwa.

Tun da farko dai ‘yan takara 7 ne suka nemi kujerar shugabancin hukumar, to sai dai ‘yan takara 5 sun janye daga takarar kafin soma zabe da safiyar yau Assabar.

Samuel Eto'o yana kada kuri'a a zaben shugabancin hukumar kwallon Kamaru
Samuel Eto'o yana kada kuri'a a zaben shugabancin hukumar kwallon Kamaru

Eto'o mai shekaru 40, da ya taka leda a kungiyoyin Barcelona, Inter Milan da Chelsea, yayi alkawarin Abubuwa da dama, duk da manufar farfado da lamurran wasannin kwallon kafa a kasar, wacce yanzu haka take fama da dambarwar zarge-zargen sama da fadi da kudade a hukumar kwallon kasar.

Daya daga cikin alkawuran da Eto ya dauka da suka fi jan hankalin jama’a, shi ne gina manyan filayen wasanni akalla 10, a cikin wa’adin mulkinsa.

A lokacin da yake bugawa kasarsa ta Kamaru wasa, Samuel Eto’o ya taimaka mata ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka sau 2 a jere, a shekarun 2000 da 2002.

A gasar ta shekara ta 2002, Eto’o ne ya lashe lambar dan kwallon da ya zura kwallaye mafi yawa a tarihin gasar, bayan da ya zura kwallaye 18.

Haka kuma a shekara ta 2000, ya jagoranci ‘yan wasan kasar suka lashe lambar zinari a gasar wasannin Olympics, bayan da ya zura kwallon a wasan karshe ta gasar.

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni

AFCON 2021, Super Eagles

Najeriya na atisaye gabanin wasanta na farko da Masar a rukunin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG