Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kusan Duniya Gaba Daya ta Kwarara Zuwa Afirka ta Kudu


Nelson Mandela
Nelson Mandela

Yau za'a fara karrama gwarzon yaki da salon mulkin nuna wariyar launin fata marigayi Nelson Mandela

Yau talata ake sa ran shugabanni daga sassan duniya daban daban zasu karrama Mr. Nelson Mandela a wani babban taron tunawa da gwarzon yaki da salon mulkin nuna wariyar launin fata, wanda ya rasu yana da shekarun haifuwa 95.

Afirka ta kudu tace shugabannin kasashen duniya fiye da 80 ne suka nuna sha’awar zasu halarci taron, da suka hada da sarakunan gargajiya da manyan wakilan gwamnatoci.

Mandela ya zama bakar fata na farko da ya shugabanci Afirka ta kudu bayan da aka daure shi na shekaru 27 saboda gwagwarmayar da yayi na yaki da salon mulkin wariyar launin fata a kasar.

Cikin shugabanni da ake sa ran zasu gabatar da jawabai na tunawa da Nelson Mandela har da shugaban Amurka Barack Obama, da shugaban kasar Cuba Ra’ul Castro, da kuma ta Brazil Dilma Rousseff.

Za a yi taron ne a babban filin wasan kwalllon kafsa dake Johannesburg. An tsaurara matakan tsaro domin mutane dubu 80 da ake sa ran zasu cika dandalin wasan. A wannan wurin ne Mr. Mandela yayi fitarsa ta karshe a bainar jama’a a bikin rufe kasar cin kofin kwallon kafa ta farko da aka taba yi a nhiyar Afirka.

A cikin ayarin na Amurka baya ga shugaba Obama, har uwargidansa Michelle, tsohon shugaban Amurka George W. Bush karami, da Bill Clinton da Jimmy Carter. Tsohon shugaban Amurka kadai da yake raye da ba zai halarci bikin ba, shine George H. W. Bush. Kakakinsa yace tsohon shugaban wanda yake da shekaru 89 da haifuwa ba zai iya tafiye tafiye masu nisa ba yanzu.
XS
SM
MD
LG