Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Miyetti Allah Ta Kama Barayin Shanu a Legas


Shanun sata da aka kwato daga barayi

Shugabannin kungiyar makiyaya wato Miyetti Allah sun gano wasu shanu da aka sato daga jihar Katsina a Legas

A wani taron manema labarai da shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa Alhaji Muhammad Kiro ya kira tare da jami'an tsaro, an gabatar da mutane uku da ake zargi da sato wasu shanu daga jihar Katsina.

Alhaji Kiro ya yi bayani. Yace shanun da aka kama an satosu ne daga garin Safana. Jihar Katsina da ma tana da babbar matsala ta sace shanu da kashe Fulani makiyaya. Jami'an tsaro suna tara shanun da aka gano amma wasu masu shanun an kashesu.

Yace sun gano shanu 29 da aka sato daga Safana. An satosu ne cikin shanu da suka fi guda dubu.

Mutanen da ake zargi kowannensu ya musanta zargin ya bada wasu dalilai daban.

Shugabannin Miyetti Allah sun fada cewa zasu mayarda shanu Safana a jihar Katsina inda za'a gudanar da cikakken bincike domin a gano duk wadanda ke da hannu a lamarin.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG