Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Basu Gamsu Da Gwamnatin Tarayya Ba Akan Ceto Daliban Chibok


Masu zanga-zanga akan daliban Chibok
Masu zanga-zanga akan daliban Chibok

Kungiyoyi masu yin fafitikan ceto daliban Chibok suna cigaba da yin zanga-zanga akan rashin amincewarsu da shirin gwamnatin tarayya domin ceto daliban.

Wasu kungiyoyi sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda gwamnatin tarayya take shirya ceto daliban da aka sace daga makarantar 'yan mata ta garin Chibok.

Kungiyoyin sun yi zanga-zanga domin mikawa shugaban kasar kokensu. To saidai zanga-zangar ta jawo martani kakkausa daga fadar shugaban kasa inda fadar ta kira kungiyoyin su juya akalar zanga-zangarsu ga kungiyar Boko Haram ba gwamnati ba.

Masu fafitikan ganin an ceto daliban da 'yan rajin kare hakkin Biladama tuni suka fara nuna bacin ransu da kalamun da suka fito daga fadar shugaban kasa. Malam Umar Dankani dake cikin fafitikar ganin an ceto daliban yace wadannan kalamun na gwamnati basu dace ba. Yace duk wani mai hankali yakamata yayi tur da kalamun domin sun nuna kasawar gwamnati. Nuni ne cewa ba abun da gwamnati zata iya yi. Abun da ya nuna shi ne gwamnatin bata damu da kowa ba sai abun da ya shafesu da na kusa da su. Da 'ya'yansu na ciki da sun ji zafin abun.

Amma Solomon Dalung wani dan rajin kare hakin dan Adam yace duk da kalamun basu karaya ba. Zasu cigaba da yin fafitikar kuma kalamun zai kara hura wutar kuzarin cigaban. Yace tun da lamarin ya faru gwamnatocin duniya suna cewa babu gwamnati a Najeriya. Abun da ya faru a kasar ba zai iya faruwa a wata kasa ba koma inda 'yan ta'ada ke cin karensu ba babbaka.

Gwamnan Kano Musa Kwankwaso ya danganta matsalar da rashin shugabanci nagari lamarin da yace dole ne ma a dukufa da yin addu'o'i da taimakawa shugaban kasa domin yana bukatar taimako.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG