Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Mata Sun Bukaci MDD Ta Tallafa Wajen Ganin An Tallafawa Mata A Najeriya


Ziyarar Sakataren MDD Anthonio Guterres a Najeriya.
Ziyarar Sakataren MDD Anthonio Guterres a Najeriya.

Kungiyoyin mata sun gana da babban Sakataren Majalisar Dinkin duniya Antonio Gutteresshi tare da kai koke don ya taimaka wajen tabbatar da rage matsalolin da mata ke fuskanta a kasar ta hanyar bada tallafi da kuma farkar da gwamnatin kasar.


Babban sakataren majalisar duniyar dai ya shigo Najeriya ne a ranar talata daga Jamhuriyyar Nijar inda ya fara kai ziyara jihar Borno ya gana da gwamna Babagana Umara Zullum, kan mühimman abubuwan kawo ci gaba a jihar, gana da ’yan gudun, wasu iyalan da rikicin Boko Haram ya shafa da kuma wasu tubabbun mayalan Boko Haram .

Daga bisani Antonio Gutteres ya shigo babban birnin tarayyar kasar don muhimman abubuwa da suka kunshi, ganawa da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, shuwagabannin addinai, da ma jiga-jigai a bangaren tattalin arziki.

Yayin ziyarar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Guterres a Abuja, Najeriya
Yayin ziyarar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Guterres a Abuja, Najeriya

Kazalika Guterres ya jagoranci bikin shimfida furanni a ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake birnin na Abuja domin tunawa da mutane 23 da aka kashe a harin bam da yan ta’adda suka kai kan ginin majalisar a watan Agustar shekarar 2011.

A yayin jawabinsa a lokacin taron shimfida furannin, Gutteres, yace majalisar dinkin duniya ba zata taba manta ma’aikatan ta da suka sadaukar da kan su wajen aiki wa kasar ba kuma ta na nuna jimaminta ga dangin wadanda abin ya shafa tare da mika godiya ga gwamnatin Najeriya da ta sake aikin gina ofishin majalisar don ma’aikatanta su koma bakin aiki.

A cikin wadanda suka gana da Guterres dai a ginin majalisar, akwai ministan ayyukan mata wacce ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta sa baki wajen ganin an shawo kan matsalolin da mata ke fuskanta a Najeriya musamman a fannin fyade da kuma cin zarafin mata.


A nata bayanin, shugabar matan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Dakta Betta Edu, ta bayyana cewa akwai bukatatar aiki tukuru wajen kawo karshen matsalolin da mata ke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum a kasar tare da bayyana jin dadi a game da ganawa da suka yi da Guterres kan ya mika wannan sako ga bangarorin zartarwa da na dokoki wato majalisun Najeriya.

Kungiyoyin mata, matasa, da bangaren da ba na gwamnati ba a Najeriya na daga cikin mutane da suka gana da Gutteres a ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake unguwan diplomatic drive da ke birnin tarama Abuja.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar dai ya fara ziyararsa ta kasashen Afirka uku ne a ranar Lahadi a kasar Senegal a wani bangare na rangadin hadin kan watan Ramadan, sannan ya je Nijar, kafin ya yi kwanaki biyu a Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra'uf cikin sauti:

Kungiyoyin Mata Sun Gana da Guterres-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
Ziyarar Babban Magatakardan MDD Anthony Guterres a jihar Borno
Ziyarar Babban Magatakardan MDD Anthony Guterres a jihar Borno

XS
SM
MD
LG