Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban MDD Ya Yi Kira Ga Sojojin Burkina Faso, Guinea, Mali Su Mika Mulki Ga Farar Hula


Babban magatakardar MDD Antonio Guterres
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira a jiya Lahadi ga hukumomin soja a Burkina Faso, Guinea da Mali su mika mulki ga farar hula cikin gaggawa, ya kuma tunatar da duniya da ta cika alkawuran “yanayi na gaggawa".

Da yake magana bayan ganawarsa da shugaban kasar Senegal Macky Sall a Dakar, ya ce sun amince da bukatar ci gaba da tattaunawa da mahukuntan dukkanin kasashen uku domin a dawo da "tsarin mulki" cikin gaggawa.

Dukkanin kasashen uku, wadanda ke fafutukar da mayakan jihadi a yankin Sahel, sun fuskanci juyin mulkin kwanan nan: Mali a watan Agustan 2020 da Mayu 2021; Guinea a watan Satumba 2021; da Burkina Faso a cikin Janairu 2022.

Sall dai shi ne shugaban kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka, wadda ta dakatar da dukkan kasashen uku daga cikinta.

Kungiyar ECOWAS ta kakabawa Mali takunkumi mai tsanani a watan Janairu bayan da gwamnatin da ke can ta ki amincewa da gaggauta komawa mulkin farar hula.

Ta kuma yi barazanar sanya wa kasashen Guinea da Burkina Faso irin wannan takunkumi idan har suka kasa ba da damar mika mulki cikin gaggawa zuwa ga farar hula cikin dan wani lokaci.

Amma gwamnatocin sojoji a kasashen biyu sun yi watsi da jadawalin da kungiyar ECOWAS ta gindaya.

XS
SM
MD
LG