Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Zai Kai Ziyari Kasashen Najeriya, Nijar, Da Senegal


Antonio Guterres
Antonio Guterres

Mataimakin kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Farhan Haq ya ce babban sakataren ya isa kasar Senegal da yammacin jiya Asabar, zai kuma tafi Nijar a ranar Litinin da kuma Najeriya ranar Talata sannan kuma ya koma New York.

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya kama hanyar ziyartar yammacin Afirka ne a jiya Asabar, domin halartar taron Musulmin da ke gudanar da bukukuwan karshen watan Ramadan, da kuma bayyana irin tasirin yakin Ukraine a nahiyar Afirka, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a ranar Juma’a.

Mataimakin kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Farhan Haq ya ce babban sakataren ya isa kasar Senegal da yammacin jiya Asabar, zai kuma tafi Nijar ranar Litinin da kuma Najeriya ranar Talata, sannan kuma ya koma New York.

Guterres zai kuma halarci bukukuwan sallar Eid al-Fitr na karshen watan Ramadan tare da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, in ji Haq, kuma yana shirin ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A cikin kasashen uku, babban sakataren zai kuma gana da wakilan kungiyoyin fararen hula, da shugabannin addinai da kuma iyalan wadanda tashe-tashen hankula da rashin zaman lafiya ya shafa a yankin Sahel na Afirka, da suka hada da 'yan gudun hijira, in ji kakakin MDD.

Guterres zai kuma gane ma idonsa tasirin sauyin yanayi kan al'ummomin da ke da rauni, kuma zai tantance ci gaba da kalubalen murmurewa daga cutar COVID-19, in ji Haq.

Babban sakataren ya fitar da wani rahoto a wannan watan yana mai cewa yakin da Rasha ke yi da Ukraine na yin barazanar durkusar da tattalin arzikin kasashe masu tasowa da dama a Afirka da ma sauran wurare da a yanzu ke fuskantar tsadar abinci da makamashi da kuma matsalolin kudi.

XS
SM
MD
LG