Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Daliban Chibok Ya Fara Zama a Abuja


Masu zanga zanga akan daliban Chibok
Masu zanga zanga akan daliban Chibok

Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa na lalubo hanyar da za'a bi a kubuto yara mata da aka sace daga Chibok ya fara zamansa a birnin Abuja.

Yayin da wasu 'yan Najeriya ke shakkar tasirin da kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa akan daliban da aka sace, sai gashi ya fara zamansa a Abuja birnin dake da tazarar daruruwan kilimita daga inda lamarin ya faru.

Al'ummomin arewa maso gabas sun fara tofa albarkacin bakinsu akan kafa kwamitin. Bulama Mali Gubyo daya daga cikin dattawan Borno yace kafa kwamitin bashi da ma'ana balantana anfani. Shin wai kwamitin din wanda ya kunshi mutanen dake zaume a Abuja kawai menene zai yi. Shi kwamitin yana zama ne a Abuja. Shin 'yan kwamitin zasu nufi dajin Sambisa ne su yi farautar 'yan matan ne ko. Shin zasu zo ne su ziyarci iyayen yaran ko kuma zasu zo su zauna a cikin garin Chibok ne. Bulama yace duk cikin rayuwarsa bai taba ganin kwamitin da bashi da ma'ana ba irin wannan kwamitin.

Ya cigaba da cewa mutane ne aka sace kuma an san inda aka nufa dasu. Gwamnati dake da sojoji da 'yan sanda me yasa ba zata shiga dajin ba ta nemesu. Yace batun cewa ba'a san adadin yaran da aka sace ba maganar banza ce domin ko yarinya daya aka sace dole a nemeta. Abu na biye dashi lokacin da 'yan ta'ada suke rigima a yakin Neja Delta ba'a taba kirawo wani gwamna ba ko jami'in 'yansanda ko shugaban wata karamar hukuma ba sai akan sace daliban Chibok. Abun da ya daurewa mutane kai shi ne menene dalilin yin hakan.Kafa kwamitin wani bata lokaci ne kawai. Abun da yakamata a yi shi ne a je a kubuto da yaran. Shi ne mafi a'ala. Shin sai an gama yankasu ko sayar dasu za'a tashi a je nemansu. A zahiri kafa kwamitin cin zarafin yaran ne da iyayensu da jihar Borno.

Ga karin bayanin Sa'adatu Muhammed Fawu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG