Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Labarin Wani Dattijo Mai Ban Tausayi


Iyayen da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace suna maida jawabi a taron da suka yi da gwamna jihar Borno, a Chibok, jihar Borno, 22 Afrilu 2014.

Wani dattijo a Najeriya yace a shirye yake ya sadaukar da kanshi da ‘yan uwanshi dattawa wadanda zasu yarda, domin musayar daliban Cibok da aka sace, a wajen ‘yan bindigan da suka sace su. Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta tattauna da wannan dattijo.

“Sunana Ibrahim Abdulkadir, ni tsohon ma’aikacin gwamnati ne, nayi ritaya tun 1993, amma ina zaune a Abuja.

Ina gani shawarar da zan bayar, tunanina yanda nake gani, a dukka kasashen duniya, da kuma masu addinin Kirista da Musulunci, dake kasashen duniya iri-iri, ire-iren mu, wanda suka kai shekaru 70 zuwa sama, ana kallonmu dattawa ne masu tunani da kuma.. mu yanzu ma mun wuce ace muna da ‘ya’ya, muna da jikoki da yawa. Irin wannan lamari na sace yara yana taba mana rai. Don bamu da karfi, babu abunda zamu iya bayarwa gudunmuwa, in banda shawara, kuma irin wannan hali idan ya taso, gwamnati kadai baza ta iya daukar duka shawararwarin warware wannan matsala ba. Ana bukatar irin mu, muyi tunani. Sai naga wata kila zai taimaka wajen cimma masalaha da wadanda suka sace yara. Idan aka samu irinmu, ni dai, da kaina zan bada kaina, kuma in samo wadanda suka kai shekaru na masu jikoki kamar ni, mai zai hana mu hada kanmu, mu wajen 200 da wani abu, Ina sadaukar da kaina a dauke mu, idan an samu irin ‘yan uwana kamar 200 ko sama da haka, mu tafi idan zai bayarda sauki ko musaya, muje muyi musaya – a bayar da mu, a sako wadannan yara. Wata kila zai zama mafi alheri, zai fi musu mai sauki, don bamu son mata, saboda mata da yara dukka hakkinmu ne. Amma mu maza bamu da sauran wani abu yanzu. Komai zamu yi, mu fitar da yarannan. Yana da kyau, muna gani yana da amfani. Shawaran da nake bayarwa kennan, kuma ni, yanzu zan fara tuntubar yawancin abokai na, wadanda suka wuce haka, zamu bude rijista mu kirga kanmu, idan mun samu dari biyu ko sama, zamu fadi adireshinmu, da wurin da ake so mu shirya, da ranar da za’a debe mu, a kaimu sannan ayi musaya da mu, a mayar da wadannan yaran kasar nan.

Da naga mata duk sun yunkura, iri-iri, sun taru, ba mata ne kadai keda wannan hakkin ba. Sai naga amfani, kamar mu da yake muna da jikoki da sauransu, bamu da karfi na jiki ko na kudi. Iyakar nuna soyayya da sadaukar da kan da zamu iya yiwa ‘ya’yanmu kennan. Don, koda dana aka kama, idan zan samu a cireshi in bayarda wuyana zan yi. Saboda haka, wadannan ma da aka sace, ‘ya’yanmu ne. Bai kamata mu bar nauyin nan, ga iyayensu ba, ko gwamnati ita kadai. Dukkanmu abun ya shafe mu. Duk inda zamu bi, mu fitar da ‘ya’yan kasar nan, ba wai lallai sai namu ba, ko jinin mu, duka namu ne. Kuma ba kudi muke da shi wanda zaimakawa ba, abun bana kudi bane. Idan su manufarsu cewa don su wulakanta mu ne, to maimakon a wulakanta wadannan yara, gara mu a wulakanta mu. Babu amfanin mu dauki mata da yara mu barsu, iyakan abunda zamu iya karesu kennan, sai kuma addu’o’in da ake yi, sune kadai zasu iya taimakawa. Amma wannan zai nuna irin damuwar da muke nunawa, da kuma soyayya ga ‘ya’yanmu, da sauran jama’ar kasa. Kuma ina fata duka mutane zasu yi tunani. Wadanda suka ga wannan shawara, zamu nemi sunayensu da adireshinsu, mu samu kamar 200 ko sama da haka, dai-dai gwargwadon yaran nan da aka sace, ana iya kaimu, a yi musaya, wata kila zasu karbi wannan shawara. Allah Ya sa a samu dacewa.”

Wannan dattijo yayi wannan bayani ne Laraban nan, a gaban gungun matan dake zanga-zangar lumana ta dirshen, a birnin Abuja a lokacin da wannan dattijo ya bada wannan shawara da ta saka da yawa daga cikin matan share hawaye.

Jama’a a duk fadin duniya yanzu haka suna zuba idanu su ga ta yaya gwamnatin Najeria zata hada kai da sauran kasashen ketare domin fito da wadannan dalibai mata ‘yan makarantar Cibok da aka sace sama da makonni uku kennan.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG