Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Nemi Kwamitin Sulhun MDD Ya Amince Da Karawa Koriya Ta Arewa Takunkumi


Amurka na kiran da a hanzarta amincewa da daftarin kudurin Majalisar Dinkin Duniya a yau dinnan Asabar, da zai sa Koriya Ta Arewa asarar dala biliyan 1 a shekara guda, daga cikin kudaden shigar da ta ke samu, wadanda da su ta ke gudanar da shirye-shiryenta na nukiliya.

Wannan mataki na karin takunkumi ya biyo bayan gwada makami mai linzami mai iya tashi daga nahiya zuwa nahiya da Koriya Ta Arewar ta yi a ranakun 3 da 28 na watan nan na Yuli, wanda ya nuna cewa wannan kasa tsananin manufa na iya auna Amurka da Turai da kamanta.

Jami'an diflomasiyya sun ce bayan kwashe makwanni ana tattaunawa tsakanin Amurka da China, Kwamitin Sulhu na MDD ya tsaida karfe 3 na yammacin yau dinnan Asabar don kada kuri'a, bayan da dukkannin mambobin kwamitin 15 sun gani sun kuma tattauna kan kudurin.

A cewar wani jami'in diflomasiyya da ke da masaniya game da wannan tattaunawar, muddun aka kada kuri'ar amincewa da kudurin, zai hana Koriya Ta Arewa sayar da kashi daya cikin uku na kayan biliyan uku da ta kan sayar. Kudurin ya auna sassa hudu wata gawayin kol, da tama da karafa da kuma kifaye da dangoginsu da Koriya Ta Arewar ke samun kudi akai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG