Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararrau Akan Sufuri Sun Yi Taro a Yamai Akan Tabarbarewar Hanyoyin Motoci a Kasashen Yammacin Afirka


Wata hanyar mota da ruwa ya mamaye

Kwararru akan harkokin sufuri daga kasashen yankin sahel dake yammacin Afirka sun yi taro waiwayen baya a Yamai akan dokar takaita kayan da motocin sufuri ke dauka da zummar sanin yadda dokar ta yi aiki da sanadin tabarbarewar hanyoyin motocin a yankin.

Waiwaye akan wasu matakan da aka dauka akan magance wasu matsalolin dake haddasa tabarbarewar hanyoyin sufuri a kasashen yammacin Afirka shi ne a kan gaba a taron kwararrun da ake yi a Yamai kamar yadda Alhaji Mustapha Kadi Umani jami’in ma’aikatar sufurin Nijar ya fada.

Yace maimakon idan an gina hanya ta yi shekara 25, sau tari bata wuce shekara 5 ta lalace dalili ke nan da taron zai saurari kowace kasa ya ji abun dake faruwa.

Musamman taron zai so ya san ko ana anfani da dokar da aka tsayar can baya na cewa a hana motoci daukan kaya fiye da ka’ida. Alhaji Mustapha yace kasashen dake taimaka masu sun nanata masu cewa idan basu dauki matakan kare hanyoyinsu ba zasu daina bada taimakon kudaden gina hanyoyin.

Bayanai sun nuna da cewa jamhuriyar Nijar ce kadai ta soma aiki da dokar kayyade nauyin kayan da motaoci zasu dauka tun daga lokacin da kasashen suka bullo da dokar.

Ministan manyan gine-gine Kada Bilai na Nijar na ganin akwai bukatar kasashe su hada kai domin kayyade girman motocin dake dakon kaya yayinda ya zama wajibi a karfafa binciken motocin tun daga tasoshin jiragen ruwa.

Wakilin jamhuriyar Benin, yace ci gaba da wayar da kawunan masu hannu a sha’anin dakon kaya a kasashen sahel wata hanya ce da zata taimaka kasashen su soma aiki da tsarin da aka fito dashi can baya.

A saurari rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG