Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Na Ci Gaba Da Yin Kiran a Saki Wani Mawaki Da Yayi Wakar Batanci


Karima Bennoune
Karima Bennoune

Kwararrun da ke kare hakkokin bil’ada masu zaman kansu a Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga mahukuntan Najeriya da su saki wani matashin mawaki Musulmi da aka yanke wa hukuncin kisa bisa zargin ya yi wata wakar batanci.

Hukumar da ke sa ido kan ‘yancin addinan kasa da kasa ta Amurka da ake kira USCIRF a takaice, ta bayyana Yahaya Sharif-Aminu a matsayin mai yin wakokin addini a jihar Kano da ke arewacin Najeriya kuma dan darikar Tijaniyya ne. Wata kotun shari’ar musulunci ta yanke wa mawakin mai shekaru 22 hukuncin kisa a watan Agustan da ya gabata saboda ya yi wata waka ta dandalin WhatsApp inda “ya yabi wani limamin darikar Tijaniya mai suna Ibrahim Niasse har ta kai ga ya daukaka shi gaban Annabi Muhammadu, “a cewar USCIRF.

Kwararrun hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya da ke bada rahotanni da shawarwari kan saba hakkokin bil’adama sun ce wasu gungun mutane sun kona gidansu Sharif-Aminu a ranar 4 ga watan Maris bayan da ‘yan siyasar yankin suka bukaci a kashe shi.

Kwararrun hukumar ta USCIRF sun ce "suna da damuwa matuka game da rashin bin doka da tsari a shari'ar Sharif-Aminu, ciki har da tsare shi ba tare da bashi damar Magana da wani ba ko daukar lauya a yayin shari'arsa ta farko, wadda ba wanda ya san lokacin da aka yi ta.

Daya daga cikin kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya, Karima Bennoune, mai ba da rahoto na musamman a bangaren hakkokin al'adu ta ce, "aiwatar da hukuncin kisa kan bayyana wani abu ta hanyar zane-zane, rubutu ko yin waka ta yanar gozo ya saba wa dokokin kare hakkokin bil’adama na kasa-da-kasa sosai da kuma tsarin mulkin Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG