Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru sun Bayyana Kalubalen Aikin Jarida A Najeriya


Wani dakin watsa labarai na zamani

Kwararru sun bayyana cewa idan aka sake lale, kafofin yada labarai na cikin gida a Najeriya suna iya buga kirji a gaban takwarorinsu na kasashen ketare da a halin yanzu suka fi su kwarjini.

Masu kula da lamura sun bayyana cewa, tuni kafofin sadarwa suka fara yunkurowa wajen samar da labarai masu sahihanci a kan lokaci, tare kuma da kyakkyawan amfani da na’urorin zamani.

Sai dai kuma sun ce ba za a iya cimma wannan burin ba sai gwamnatoci sun zage damtse wajen samar da yanayin da ya dace da kuma kayan aiki da zai ba jama’a zabi.

A jawabinsa wajen wani taron bunkasa aikin jarida da akayi a Gombe, Professa Pate shugaban tsangayan koyon aikin jarida na jami’ar Bayero dake Kano ya bayyana cewa, akwai kalubala dake gaban ‘yan jarida da kuma gwamnatoci na cimma muradan aikin. Yace zamanin yin abinda dan jarida yaga dama ya wuce, yace idan basu sake lale ba, zasu rasa masu sauraro, kuma masu tallace tallace suma su guje su abinda zai iya durkusar da kafofin sadarwa da suke yiwa aiki.

A bangaren gwamnati kuma, Prof. Pate yace illar rashin inganta kafofin sadarwar shine, mutane zasu rika sauraron radiyo mai jini dake yayata labaran karya wanda zai iya jefa al’umma cikin rudani.

Ga ratohon da wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Mohammed ya aiko daga Bauchi:

Kalubalar Aikin Jarida-3:30
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG