Accessibility links

An Yi ma Daruruwan 'Yan Sanda Karin Girma a Najeriya


'Yan Sandan Najeriya su na fareti

Daga cikin 'yan sanda fiye da dari biyar da suka samu karin girma, kimanin 140 sun fito ne daga rundunar 'yan sanda ta Jihar Oyo.

Rundunar 'yan sandan Najeriya da hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kasa sun yi karin girma ma daruruwan 'yan sanda a Najeriya.

A lokacin da yake daurawa 'yan sandan da suka samu karin girma sabbin mukamansu a hedkwatar 'yan sanda ta Jihar Oyo, Kwamishinan 'yan sanda Mohammed Abdulqadir Indabawa, ya ja kunnen 'yan sandan da su kara kwazo su kuma rike aikinsu cikin amana, yana mai fadin cewa a matsayin jihar Oyo ta fi kowace jiha samun wadanda aka yi ma karin girma, haka kuma za a bukaci 'yan sandan jihar su nuna kwazo fiye da saura.

Yace dacewarsu ta sa suka samu wannan karin girma, don haka yana rokonsu da su ci gaba da zamowa abin misali.

Daya daga cikin wadanda suka samu karin girma, Sufeto A. Gideon, wanda ya samu karin girma zuwa ASP, ya bayyana murnar karin girma da ya samu, yana mai bayyana cewa aiki da juriya da hakuri, da kuma yin aiki mai kyau tsakani da Allah yana da ranarsa, kuma ranar ce suka gani.

'Yan sanda kimanin 500 suka samu karin girma a Najeriya, kuma kimanin 140 daga cikinsu sun fito ne daga rundunaer 'yan sanda ta jihar Oyon.

XS
SM
MD
LG