Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyoyin Gwamnati A Amurka Sun Bukaci Kotu Ta Daure Cohen


Shugaba Donald Trump da tsohon lauyansa Michael Cohen
Shugaba Donald Trump da tsohon lauyansa Michael Cohen

Lauyoyin gwamnati a nan Amurka sun fada a jiya Juma’a cewa tsohon lauyan shugaba Donald Trump, Michael Cohen ya cancanci a yanke masa hukuncin zaman gidan yari.

Wannan shawarar na kunshe ne a cikin karar da lauyoyin suka gabatarwa kotu kafin a yanke masa hukunci a mako mai zuwa a New York.

Cohen ya amince da laifinsa na aikata ba daidai ba kuma ya baiwa binciken da hukumomin jiha da na tarayya suka gudanar watanni da watanni hadin kai, ciki har da ganawa sau bakwai da ya yi da mai bincike na musamman Robert Muller.

Masu shigar da karar sun ce sashen kimanta hukunci na kotu, yace tsarin tabbatar da hukuncin tarayya ya nuna Cohen zai iya zaman akalla shekaru hudu a gidan yari. Lauyoyin gwamnatin sun ce kiyasin hukuncin na tabbatar da girmar laifin da Cohen ya aikata cikin ganganci.

Masu shigar da karar sun ce bai kamaci a yiwa Cohen sassaucin da aka saba yiwa wadanda suka baiwa bincike hadin kai ba, yayin da suke bada dalilansu bisa amincewarsa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG