Accessibility links

Likitoci a Kasar Nijar Sun Dauki Matakan Kiyaye Cutar Yoyon Fitsari


Wasu mata su na hutawa bayan da aka yi musu tiyatar magance yoyon fitsari

Ganin yada matan dake fama da cutar yoyon fitsari ke karuwa, likitoci a hukumar Maradi, ta jimhuriyar Nijar, sun dukufa wajen fadakar da mata hanyoyin da za su bi domin kaucewa kamuwa da cutar.

Ganin yada matan dake fama da cutar yoyon fitsari ke karuwa, likitoci a hukumar Maradi, ta jimhuriyar Nijar, sun dukufa wajen fadakar da mata hanyoyin da za su bi domin kaucewa kamuwa da cutar.

Cutar yoyon fitsari cuta ce wadda ke faruwa idan aka sami haihuwa mai wahala. Akan kama cutar kuma ta wajen yankan gishiri da guryi, ta gargajiya, da ake yi a kauyuyuka.

Wata mata mai shekaru 70 da ke fama da wannan cutar har shekaru 20 tace abin da ya jawo mata wannan cuta shine haihuwar ta na takwas. Ta ce rashin likita a kusa da inda suke da ta shiga nakuda shi yasa ta kamu da cutar.

Gwamnati tana talafawa mata masu wanan cuta ta wajen samar masu da magani kyauta, da aiki, da abinci. An kuma kafa wani sashe musaman domin kula wa mata masu fama da cutar.

Wani likita a Nijar, Dr. Inusa Mohammed, yayi bayani cewa ba su bata lokaci idan suka ga mace ta zo da ta nuna alamar baza ta iya haihuwa da kanta ba. Ya bayana cewa idan mata ta zo tana fama haka, sukan yi hanzarin taimaka mata ta haihu domin kiyaye kamuwa da cutar yoyon fitsari.

Ga Choibu Mani da cikaken bayani.

XS
SM
MD
LG