Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaran Makarantun Firamare a Carlow Zasu Taimakawa Yaran Najeriya a Yaki da Polio


Yara a kasar Ireland
Yara a kasar Ireland

Makarantun firamare na Carlow a kasar Ireland zasu giudanar da aikin gasar zane-zane don tara kudin sayen maganin rigakafin Polio da za a ba yara ‘yan’uwansu a Najeriya

Makarantun firamare na Carlow, a yankin karamar hukumar carlow ta kasar Ireland, zasu shiga sahun masu tallafawa wani sabi=on shirin Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, na samar da maganin rigakafin cutar shan Inna ko Polio ga yara ‘yan’uwansu a Najeriya da ma wasu kasashen dake fama da wannaqn cuta mai gurguntawa.

An gayyaci yaran makarantar da su gabatar da zane-zane da za a iya yin amfani da su wajen karfafa sakon kyamfen yaki da Polio, inda zane-zanen kowane yaro zai taimakawa asusun UNICEF wajen samun kudin sayen maganin rigakafin cutar Polio da niyyar kare wani yaron dagfa kamuwa da ita.

Wani kamfanin hada-hadar ayaba a kasar Ireland mai suna Fyffes, shi ne yake daukar nauyin wannan gangami, inda ake fata makaranatu da dama a Carlow zasu shiga sahu.

A tsakiyar watan nan na Maris za a aike da cikakken bayanin wannan gasar zane-zane ga makarnatun yankin, kuma dukkan zane-zanen da suka yi nasara, to za a buga su domin amfani wajen yayata wannan shiri na yaki da Polio a duk fadin kasar Ireland.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG