Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UEFA: Madrid Ta Fitar Da Sunayen ‘Yan wasan Da Za Su Kara Da Liverpool


Manajan Read Madrid, Zinedane Zidane

Madrid za ta je wasan ne da zaratan ‘yan wasa 21, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid​ ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasanta da za su fafata da abokanan hamayyarasu na Liverpool a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

A ranar Talata Madrid za ta gwada kaiminta da Liverpool a wasan farko na zagayen quarterfinals a filin wasa na Estadio Alfredo Di Stefano da ke birnin Madrid a kasar Spain.

Karin bayani akan: Real Madrid​, Liverpool, Sergio Ramos, da Benzema.

Za ta je wasan ne da zaratan ‘yan wasa 21, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin.

Ga jerin ‘yan wasan:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Altube

Masu tsaron baya: E. Militao, R. Varane, Nacho, Marcelo, Odriozola da F. Mendy

‘Yan wasan tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, Valverde, Isco da Arribas

Masu kai hari: Benzema, Asencio, Lucas V., Vini Jr., Mariano da Rodrygo.

Yanzu haka, dan wasan tsakiya Fede Valverde ya dawo daga jinya, amma Eden Hazard, Sergio Ramos da Dani Carvajal ba za su samu damar buga wasan ba.

Masu fashin baki sun ce babban kalubalen da ke gaban Madrid shi ne, yadda za su kare bayansu lura da cewa ‘yan wasan Liverpool sun kware wajen kai hari.

UEFA Da FIFA Ba Sa Kyautawa ‘Yan Wasa - Pep Guadiola

UEFA Da FIFA Ba Sa Kyautawa ‘Yan Wasa - Pep Guadiola
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG