Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liverpool Ta Sha Ci Daya Mai Ban Haushi A Southampton


Dan wasan gaba na Liverpool Mohammed Salah.

Kungiyar Liverpool da take kan gaba a wasannin Firimiya Lig, ta sha kashi a hannun Southampton a jiya Litinin.

Cira kwallo da Danny Ings ya yi a kan golan “The Reds” Alisson, bayan bugun tazarar da James Prowse ya dauko, shine ya fada raga ya kai Southampton ga yin nasara a kan tsohuwar kungiyarsa.

Liverpool da Jurgen Klopp ke horar da ita, wannan shi ne karo na biyu da ta sha kashi a wannan kakar wasa, amma kuma tana ci gaba da darewa a kan kungiyoyin Firimiya Lig da ratar kwallaye kana maki biyu kacal ne kawai ta samu a cikin maki tara a baya.

Su ko Manchester United da Manchester City duk wanda zai yi nasara a wasanninsu da suka rage, za su kara cira gwarazan na yanzu ne.

Nasarar farko da Southampton ta yi a cikin wasannin Firimiya lig biyar ya kai ta ga matsayi na shida a cikin jerin kungiyoyin wasan.

Ko shakka babu masu masaukin bakin sun taka leda kana suka saka kwallo a farkon wasan, lamarin da ba saban ba ne ga Liverpool kana suka rike dan wasan tsakiyar “The Reds” Jordan Henderson kuma suka tsare gida yayin da bakin nasu ke dannawa a gidansu.

Karin bayani akan: Liverpool​, Manchester United​, Manchester City​, da Premier League.

Dubi ra’ayoyi

Diego Maradona 1960-2020
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00
Karin bayani akan Diego Maradona
XS
SM
MD
LG