Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Ceto Na Ci Gaba Da Zakulo Jama'ar Da Ambaliyar Tabo Ya Hallaka


Masu ayyukan ceto na ta tona cikin baraguzai da laka tun daga jiya Lahadi, a yinkurinsu na neman mutane bayan da wani dinbin ruwa ya malalo daga koguna uku masu ambaliya a Colombia, ya malale yankin da dare, inda ya lalata gidaje da madafun harkoki, ya kuma hallaka mutane wajen 200.

Nan da nan bayan da gabobin kogunan su ka farfashe, sai gocewar laka ta yi kaca-kaca da garin Mocoa, da ke kudu maso yammacin kasar.

Shugaba Juan Manuel Santos, ya ziyarci garin da ya yi kaca-kaca mai dauke da mutane 40,000, wanda ke daura da kan iyakar Ecuador, ranar Asabar sannan ya ayyana yanayin a matsayin bala'in da ya abka ma jama'a.

Santos, ya yi gargadin cewa mace-macen na iya karuwa, sannan ya kara da cewa, "Ba mu san adadin wadanda abin zai rutsa da su ba."

A nasu bangaren kuwa, jami'an kungiyar agaji ta Red Cross sun ce mutane akalla 203, sun samu raunuka a wannan al'amarin, baya ga mutanen da ba a san adadinsu ba da har yanzu ba a gansu ba.

Hotunan bidiyo da aka dauko na wurin na nuna gine-gine sun fadi, da tarkacen motoci, itatuwa sun faffadi, yayin da mazauna wurin, wadanda ke ciki alamar tashin hankali, ke ta kai komo, su kuma masu ayyukan ceto ke ta zakulo wadanda su ka ji raunuka da kuma gawarwaki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG