Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Kamfanonin Mai A Najeriya Za Su Shiga Yajin Aiki A Mako Mai Zuwa


Zanga-zangar Lumana Ta NLC
Zanga-zangar Lumana Ta NLC

Daya daga cikin manyan kungiyoyin man fetur da iskar gas a Najeriya za ta shiga yajin aikin da za a fara daga ranar 3 ga watan Oktoba a fadin kasar domin nuna adawa da manufofin gwamnati da ke janyo wa 'yan Najeriya kuncin tabarbarewar tattalin arziki, in ji shugabannin kungiyoyin a ranar Alhamis.

Najeriya ita ce kasa mafi arzikin man fetur a nahiyar Afirka kuma ta dogara da kayayyaki kusan kashi 90% na kudaden da ake samu daga kasashen waje da kusan rabin kasafin kudinta.

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG) ta umurci mambobinta da su tabbatar da bin ka’idar yajin aikin sai-baba-ta-gani da manyan kungiyoyin ma’aikatan Najeriya biyu suka kira.

Kungiyar Maikatan Man Fetur, NUPENG
Kungiyar Maikatan Man Fetur, NUPENG

Kungiyar ta NUPENG tana wakiltar dimbin ma’aikata ne a sassan mai da iskar gas, wadanda suka hada da ma’aikatan tankunan mai, da direbobin tankar mai da masu aikin famfo a gidanjen mai, kuma matakin da ta dauka na shiga yajin aikin wani gagarumin ci gaba ne na takaddamar kungiyoyin da gwamnati. .

Shugaban kungiyar ta NUPENG Williams Akporeha ya ce manufofin gwamnati sun haifar da "zama mai raɗaɗi da kuncin zamantakewar tattalin arziki" ga 'yan Najeriya ba tare da wasu matakan da za su bi don rage radadin da kuma tasirin nan take ba."

Shugaban kasa Bola Tinubu dai yana cikin sha matsin lamba kan ya janye matakin da ya dauka na soke tallafin man fetur wanda ya yi sanadiyar kudin mai ya yi kasa ciki shekaru da dama da suka gabata amma kuma ya daura wa kudaden gwamnati nauyi.

Yayin da manufofinsa ke faranta wa masu zuba hannun jari rai, kungiyoyin kwadagon sun ce lamarin ya haifar da tashin gwauron zabi ga ‘yan Najeriya – kimanin hudu cikin 10 daga cikinsu suna rayuwa kasa da kangin talauci a kasar yayin da suke fama da hauhawar farashin kayayyaki a kusan shekaru ashirin.

~ REUTERS

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG