Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magudun Adawa a Kenya Raila Odinga, Ya Bukaci a Sake Gudanar da Zaben Shugaban Kasa


Raila Odinga, madugun adawar Kenya
Raila Odinga, madugun adawar Kenya

Raila Odinga madugun adawar siyasar Kenya ya bukaci a sake gudanar da zaben shugaban kasar cikin kwanaki 90domin shawo dambarwar siyasar kasar wadda a ganinsa ta sa kasar cikin wani hadari

Jagoran ‘yan adawar Kenya Raila Odinga ya bukaci a gudanar da sabon zaben Shugaban kasa cikin kwanaki 90, ya ce kasar na fuskantar matukar hadari sanadiyyar dambarwar siyasa.

Odinga ya zanta ne da kafar labarai ta Associated Press kwanaki uku bayan da ya kaurace wa zagaye na biyu na zaben Shugaban kasa da aka sake gudanarwa bayanda aka soke na farko da akayi a watan Agusta, wanda Kotun Kolin Kasar ta yi watsi da sakamakonsa saboda magudi.

Odinga ya ce zaben na ranar Alhamis haramtacce ne saboda Shugaba Uhuru Kenyatta bai kara da kowa ba.

Odinga ya zargi jami’an diflomasiyyar Amurka da na sauran kasashen yanmacin duniya da nuna rashin yakamata saboda shawarar da su ka bayar ta gudanar da zagaye na biyu na zaben ranar Alhamis.

Bayan da aka kirga kusan dukkannin kuri’un da aka jefa a zaben baya-bayan nan, Hukumar zaben ta ce Kenyatta ya samu kuri’u miliyan 7, adadin da Odinga ya ce ba shakka choge ne idan aka yi la’akari da rashin fitowa zaben da aka yi.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG