Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maganar Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako Ta Farko Tunda Ya Gudu Kasashen Waje.


Murtala Nyako, tsohon gwamnan Jihar Adamawa
Murtala Nyako, tsohon gwamnan Jihar Adamawa

A karon farko tun bayan da Murtala Nyako ya sulale zuwa kasashen waje, biyo bayan farautarsa da hukumomin Najeriya suka yi, awowi kadan da tsige shi, tsohon gwamnan jihar Adamawa, ya bayyana halin da yake ciki, tare da bayyana aniyarsa ta komowa gida Najeriya.

Nyako, wanda tsohon soja ne, ya arce zuwa kasar waje ne bayan da hukumomin Najeriya suka yi barazanar cafke shi, bisa zargin da yan majalisar dokokin jihar suka yi masa na almundahana da kudaden jihar, yayin da wasu ke danganta lamarin da budaddiyar wasikar daya rubuta na zargin da yayiwa shugaban kasar Goodluck Jonathan, da cewa yana yakin kare dangi ga’yan arewa.

A dai watan Yuli ne, yan majalisar dokokin jihar suka tsige shi, kuma tun lokacin ba’a san inda ya shiga ba. Saurari tabakin Nyako

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

XS
SM
MD
LG