Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Hana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa


Wata mai goyon bayan dan takara Mohammed Nasheed dauke da kwali lokacin zanga-zangar nuna kin jinin 'yan sanda da suka hana gudanar da zabe

'Yan sandan Tarayyar Tsibiran Maldives sun kewaye ofishin hukumar zabe yau asabar, suka hana jami'ai rarraba kayayyakin zaben da aka shirya gudanarwa

‘Yan sanda na tarayyar tsibiran Maldives sun hana jami’an zabe na kasar gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka shirya yi yau asabar, abinda ya haddasa damuwa a kasashen ketare.

Wani kakakin rundunar ‘yan sandan kasar, Abdullah Nawaz, yace an hana hukumar zabe gudanar da wannan zaben ne a saboda jami’anta sun kasa bin umurnin da kotu ta bayar cewa dukkan ‘yan takara su amince da kundin rajistar sunayen masu jefa kuri’a kafin a gudanar da shi.

Kwamishinan zabe na kasar Maldives, Fuwad Thowfeek, yayi kokarin gudanar da wannan zabe kamar yadda aka shirya. Amma yace ‘yan sanda sun kewaye ofisoshin hukumar zaben yau asabar suka hana a rarraba kayayyakin zabe.

Indiya ta ce ta damu matuka cewa an kasa gudanar da wannan zaben shugaban kasa duk da cewa kotu ta bayarda umurnin a gudanar da shi.

Tarayyar Maldives kasa ce wadda akasarin al'ummarta Musulmi ne, kuma ta kunshi wasu kananan tsibirai kimanin dubu daya da dari biyu dake warwatse cikin tekun Indiya, a kudu maso yamma da kasar Sri Lanka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG