Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Shari'a Ayo Salami Ya Karyata Labarin Da Lauyoyin Magu Suka Yada Cewa Ya Yi Nadamar Karbar Aikin Da Yayi


Ibrahim Magu
Ibrahim Magu

Shugaban kwamitin Shugaban Nigeria Mai binciken badakalar da ake zargin Mustafa Ibrahim Magu ya tafka a hukamar yaki da cin hanci da rashawa, Justice Ayo Salami ya karyata labarin da lauyoyin Magu suka yada na cewar wai yayi nadamar kar’bar aikin.

Mai Shari'a Ayo Salami wanda ke shugabancin wannan kwamitin yayi tir da Allah wadai da, abin da ya kira labarin kanzon kurege da aka wallafa a cikin jaridu, wanda lauyoyin Ibrahim Magu ne suke cewa wai yayi juyayi da nadama a kan karban wannan shugabancin da aka bashi na kwamitin da ke binciken Ibrahim Magu.

Ayo Salami ya nuna mamakinsa kan yadda aka ari bakinsa aka ci masa albasa. Malam Nasiru Zahradin ƙwararre a kan fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ya ce, "Tun ba yau ba ake irin wannan buge-buge a jaridu, musamman irin jaridun nan na zamani, su suke bubbuga waɗannan labarai, mutane masu goyon bayansa da lauyoyi 'yan'uwansa suke ta sawa a kafar yaɗa bayanai domin su ga wannan kwamiti da aka kafa sun wargaza shi, sun ce abunda yake ba daidai ne ba"

Ya ƙara da cewa ya kamata hukuma ta tanadi hukunci ga masu irin wannan cin zarafi ga al'umma. A gurfanar da su gaban shari'a. Ya ce su kan su, kafofin yaɗa labarai da aka ce sun yi ta ƴaɗa labaran, wanda na kanzon kurege ne, su ma a hukunta su.

Abdulkarim Ibrahim wani ƙwararre a harkar intanet da yadda ake amfani da ita wajen yaƙi da cin hanci, ya jinjina wa Ayo Salami. Ya ce suna so ne a janye labarin da kowa ya riga ya sani, bai dace ba a ce komai ya faru sai a kai shi ga jarida, al'umma basa sanin me ake ciki sai dai a yi ta surutai a jarida a haka har abun ya wuce.

A wancan lokacin, lauyoyin na ganin suna burge shi don haka ma suka cigaba da irin wannan aikin. Amma Ayo Salami ya fahimci manufarsu, kuma ya ƙaryata cewa bai faɗi magan nan ba.

Saurara cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG