Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Son Zama Shugaban Amurka Sai Ya Sa Linzami a Bakinsa In Ji Obama


Shugaban Amurka, Barack Obama

Shugaba Obama yace dokar kasa ta bukaci gwamnatinsa ta bada bayani game da tsaron kasar, ciki har da wasu bayanai da ba su kamaci a fito da su bainar jama’a ba game manyan 'yan takarar kujerar shugaban kasa.

'Yan takarar sune Hillary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican wanda shugaba Obama ke kwatantashi da wanda bai cancanci zama shugaban kasa ba.

A gwagwarmayan yakin neman zabe da aka fara shekara daya da ya wuce, an gano Donald Trump da jawabi ga jama’a da tare da mai da hankali akan abin da aka shirya masa ya fada akan takarda.

Wanda hakan kan sa ana samun kurarai acikin maganaganunshi kuma yasa kusoshi a cikin kasar suna sukar lamirinsa kan haka.

Wannan lamari yasa jama’a na shakku akan ko Trump zai rike wasu muhimman bayabnai da za a bashi da suka shafi tsaron kasar.

Da yake bayani ga 'yan jarida a Pentagon, shugaba Obama yace in dai mutane suna so zama shugaban kasa, to ya kamata su fara rayuwa irin ta shugabannin kasa, manufa ba za su fallasa bayanan tsaron kasa da za'a basu ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG