Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Bayyana Damuwa Kan Badakalar Daukar Aiki A Najeriya


SENATOR ABDULLAHI IBRAHIM DANBABA
SENATOR ABDULLAHI IBRAHIM DANBABA

Wasu Kwamitocin Majalisar Dattawa sun dauki lokaci su na tattaunawa akan batun daukar aiki a Ma'áikatu da hukumomin gwamnati har da bangaren Jamián tsaro, inda wasu suka nuna rashin gamsuwarsu da yadda ake daukan ma'áikatan Gwamnati da yadda ake maya gurbin jamián tsaro.

Kwamitin kula da Daidato a gwamnati da harkokin gudanar da mulki da kuma Kwamitin Kula da harkokin Sojin kasa ne suka baiyana damuwarsu a kan yadda suka gano cewa ana maye guraban da aka samu a ma'áikatu da hukumomin gwamnati har da ma na jamián sojin kasa.

A lokacin da yake gana wa da manema labarai Mataimakin mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye a Majalisar Dattawa Sanata Abdullahi Ibrahim Danbaba ya ce tun a Majalisa ta 8 ya dade yana bibiyan yadda abubuwa suke tafiya musamman a bangaren jamián tsaro na sojin kasa, saboda haka yai wasu tambayoyi da bai yi wa Mataimakin Shugaban Kwamitin Kula da harkokin sojin kasa dadi ba domin ya nemi a ba shi kasidar daukan aiki da yadda ake tabbatar da daidaito. Danbaba ya ce akwai tanadetanade da kundin tsarin mulki ya gindaya amma yana ganin ba a bin shi yadda ya kamata.

Shi ma Shugaban Kwamitin kula da daidaito da harkokin gudanar da mulki Sanata Danjuma Laah, ya koka da yadda ake kayyade shekaru a cikin bukatun daukan matasa aiki. La'ah ya ce ba laifin matasan ba ne, wani lokaci yanayin karatu ne ka sa wa a dauki lokaci mai tsawo. La'ah ya ce bai kamata a kaiyade shekaru ba in har ana so matasa su samu aiki a kasa kuma haka shi ne kawai mafita.

A lokacin da ya ke nazarin abinda kundin tsarin mulki ya tanada a game da daukan ma'áikata a Najeriya, Barista Mainasara Umar ya yi bayani cewa kundin tsarin mulki yayi tanadi da zai ba kowa dama ba tare da nuna banbancin kabila ko bangare ko addini ba. Mainasara ya ce kowa yana da dama da zai taka rawa wajen gina kasa, saboda haka bin dokokin kasa shi ne mafi alfanu.

Kwamitin kula da daidaito da harkokin gudanar da mulki a majalisar dattawa ya yi kira ga Gwamnati da ta bude kafa na daukan maáikata a dukan fanoni maimako daukan maáikata a asirce.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00


XS
SM
MD
LG