Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Lauretta Onochie A Matsayin Kwamishiniyar Hukumar Zabe


Lauretta Onochie
Lauretta Onochie

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da nadin mai taimakawa shugaba Buhari, Lauretta Onochie, a matsayin kwamishiniyar hukumar zabe ta INEC.

Wannan lamari dai na zuwa ne bayan korafe-korafe daga wasu ‘yan Najeriya da suka hada da ‘yan jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararren hula kan nadin na Lauretta Onochie a matsayin kwamishiniyar hukumar INEC.

A can baya da Lauretta Onochie ta yi ikirarin ita mamba ce a jam’iyyar APC mai mulkin kasar kamar yadda wakiliyarmu a majalisar tarayyar Najeriya ta tabbatar, duk da yake daga baya an ruwaito ta tana cewa ta janye daga zama 'yar jam'iyyar.

A tanadin doka dai, ana bukatar duk wanda zai rike mukamin kwamishina a hukumar zabe ta INEC ya kasance wanda bai da siyasar bangaranci ko jam'iyya.

A halin yanzu, ana kan jiran sanarwar matakin da majalisar dattawan ta dauka a hukumance bayan tashi a zaman su na yau.

Karin bayani akan: INEC, APC, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Idan ana iya tunawa dai a makwannin baya-bayan na ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dattawan kasar wasikar neman ta tabbatar da nadin Lauretta Onochie, wacce a halin yanzu ta na daga cikin masu taimaka masa kan harkokin yada labarai, a matsayin kwamishiniya a hukumar zaben, tare da wasu mutane 3.

A yayin kare kanta kan korafe-korafen da aka shigar a kan ta na ita yar siyasa ce a lokacin aikin tantance ta a gaban kwamitin majalisar tarayya a ranar Alhamis, Lauretta Onochie ta jadada cewa ba ta cikin wata jam’iyyar siyasa kuma ba ta marawa wata jam’iyyar baya.

Ta kara da cewa ana korafi a kan ta ne saboda yadda ta ke tabbatar da cewa mutane su rika bin doka da ka'ida a duk inda su ke aiki.

Haka kuma Lauretta Onochie ta bayyana cewa, tun bayan lashe zaben da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a shekarar 2019 ta tsame hannun ta daga duk abubuwan da suka shafi siyasa, haka kuma ba ta shiga aikin sabunta matsayin mamba ba a jam’iyyar APC da ta ke a cab baya.

XS
SM
MD
LG