Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Amince Da Bukatar Buhari Ta Ciwo Bashin Dala Biliyan $5.8


Shugaba Buhari (Twitter/ Muhammadu Buhari)

A ranar Laraba ne majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na karbo bashin dala biliyan 5.8 daga kasashe masu ba da lamuni na duniya.

Kudaden da aka samu daga bankin duniya, bankin fitar da kayayyaki da shigo da kaya ta kasar China, da hadin gwiwar gwamnatin Jamus, da bankin raya Musulunci da dai sauran masu ba da lamuni, za’a bayar ne don ayyukan samar da wutar lantarki, da ruwa da tsaftar muhalli, da shirye-shiryen kawar da zazzabin cizon sauro, da ayyukan noma.

Ciyo bashin wani bangare ne na kasafin kudin shekarar 2021 don magance illar cutar korona da kuma faduwar farashin mai, wanda ya kawo cikas ga shirin kashe kudi a Najeriya saboda sayar da mai ya kai kashi 90% na kudaden da ake samu daga kasashen waje.

Ofishin kula da basussuka ya ce a ranar Talata jimillar bashin da ake bin Najeriya ya haura dala biliyan 92.75 a watan Satumba, wanda ya karu da kashi 18 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Kasar wanda mafi girman tattalin arziki a Afirka, na ta tara basussuka don samar da ayyukan samar da ababen more rayuwa da kuma habaka tattalin arzikin da ke murmurewa daga koma bayan tattalin arziki sakamakon faduwar farashin man fetur da annobar ta haifar.

Buhari ya mika kasafin Naira tiriliyan 16.39 na shekarar 2022 ga majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi. ‘Yan majalisa na iya yin sauye-sauye a kasafin kudin kafin sannan a mayar da shi ga shugaban kasa domin ya zama doka idan ya amince a yi masa kwaskwarima

XS
SM
MD
LG