Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Bankado Badakalar Naira Triliyan Uku a Ma'aikatu


Komitin Kula da Harkokin Kudi na Majalisar Dattawa a karkashin Jagorancin Sanata Solomon Adeola ya ce ya gano cewa, a cikin shekaru 5, Ma'aikatu da Hukumomin Gwamnati sun yi sama da fadi da kudade har Naira Triliyan 3 wadanda ba a sa su a cikin lalitar Gwamnati ba.

Manyan Hukumomi Sama da 60 masu samar da kudaden shiga da ya kamata a zuba a lalitar gwamnati ne suka tafka wannan badakalar da kwamitin kudi na majalisar dattawa ya ce ya kiyasta sun kai wuri na gugan wuri naira Triliyan uku, da suka kasa biya a cikin asusun hadahadar Kudade wanda aka fi sani da CFR a turanci.

Shugaban kwamitin Solomon Adeola ya ce wannan mataki da hukumomin suka daukar wa kansu shi ne ya kasance tushen tabarbarewar kudi na gwamnati Tarrayya wanda ya haifar da dimbin bashi musamman daga shekara 2014 zuwa yau.

Daya cikin yayan kwamitin kudi a Majalisar Dattawan Yusuf Abubakar Yusuf yayi karin haske akan wannan bincike da suke yi inda ya ce sun take doka wajen kashe kudaden ba tare da neman izini daga wajen Majalisar Dokokin kasa ba, saboda haka dole ne su mayar da kudaden in ba haka ba kuma a hana gwamnati basu kudade tunda su ma suna samun nasu kudaden. Sanata Yusuf ya ce yin haka zai rage wa Gwamnati yawan kashe kudade.

A cikin kasafin kudin kasa na wannan shekara na Naira triliyan 13. 588 an amince da Triliyan 5.196 a matsayin gibi yayin da aka sake ware Triliyan 3.324 don biyan bashi wani abu da kwararre a fanin Talib arziki Shuaibu Mikati ya ce dole ne a ci bashi Domin Hukumomin Gwamnatin ba za su iya rike wa da kudaden shiga Kawai ba.

Karin bayani akan: Yusuf Abubakar Yusuf, Majalisar Dattawan, Nigeria, da Najeriya.

Shuaibu Mikati ya ce babu yadda za a yi kasar ta dogara da haraji na hukumomi da na yanKasa kawai, dole nea ciwo bashi, saida yana mai bada shawarar a rage cin bashin dayawa domin ana wakaci watashi da kudaden gwamnati a kasa, saboda haka a rika sara ana duban bakin gatari.

Kwamitin kula da harkokin kudi na Majalisar Dattawan ya ce dole hukumomin gwamnatin nan 60 su mayar da wadanan makudan kudade, domin rashin zuba su a lalitar gwamnati ya sabawa tanadin kudin tsarin mulki da dokar kula da kasafin kudi.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

XS
SM
MD
LG