Accessibility links

Majalisar Dinkin Duniya Zata Kara Sojoji Dubu Goma a Afirka ta Tsakiya


Dakarun kasashen Afirka dake kiyaye zaman lafiya a Afirka Ta Tsakiya.

A kokarin shawo kan rikicin da ya addabi Afirka Ta Tsakiya, Majalisar Dinkin Duniya ta amince ta kara sojoji dubu goma da 'yan sanda da dama.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince a fadada aikin sojojin kiyaye zaman lafiya a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Bai daya kwamitin mai wakilai goma sha biyar ya amince a tura sojoji dubu goma da 'yan sanda dubu daya da dari takwas karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

A watan satumba idan Allah ya kaimu sojoji zasu fara aikin na kiyaye zaman lafiya, zasu maye gurbin sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika.

Sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika dubu shidda da kuma sojojin Faransa dubu biyu sun kasa sha kawo tarzomar addini data kashe dubban mutane ta kuma tilaswa kimamin miliyan guda arcewa daga gidajensu.

Jiya Alhamis kwamiytin sulhu yayi na'am da kudurin tura sojojin da zasu maye na kungiyar kasashen Afrika.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch tace an bata lokaci sosai kafin aka zartar da wannan kuduri, to amma kudurin ya tanadi tura sojoji masu karfi da zasu kare farar hula, su kuma taimaka wajen daidaita al'amurra a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
XS
SM
MD
LG