Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai A Mali


Wasu da hari ya rutsa da su

An kashe akalla mutane 95 a tsakiyar Mali a jiya litinin a lokacin da 'yan bindiga suka kaiwa wani kauye hari a cikin dare, inda suka bude wuta a kan jama’a kana suka cinnawa gidajen mutane wuta.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Mali Amadou Sangho yace yanzu haka akalla mutane 19 sun bace.

Wani dan jarida a yankin ya fadawa sashen Faransanci na Muryar Amurka cewa harin ya auna kauyen Sabanetou, kusa da tsakiyar garin Mopti.

Ya kuma ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa ya haura 100.

Rahotanni da suka fara fitowa na cewa akwai yiwuwar mayakan Fulani ne suka kaiwa mazauna kauyen 'yan kabilan Dogon hari.

“Sakataren MDD Antonio Gueterres ya yi alwadai da harin, ya yi kuma kira ga kungiyoyin kasar Mali da su gujewa wa maida martini, a cawar sanarwar mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric.

Kwamitin sulhun Majlisar Dinkin Duniya ya shirya wata zaman tattaunawa a cikin wannan wata a kan yiwuwar sabonta ayyuka MDD na zaman lafiya a Mali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG