Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi gwamnatin Sudan ta Kudu da kisan gilla da yiwa mata fyade


Shugaban Sudan ta Tsakiya Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Tsakiya Salva Kiir

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da kare hakkin bil adama, ya zargi gwamnatin Sudan ta Kudu da aiwatar da wani tsarin kisa da yin fyade da kuma wawure dukikoyoyin fararen hula a lokutan da ta ke yakar ‘yan tawayen kasar.

Wani sabon rahoto da aka fitar a yau Juma’a ya nuna cewa dukkanin bangarorin da ke takaddama a kasar sun aikata laifukan cin zarafin bil adama akan fararen hula.

Amma rahoton ya ce dakarun kasar sun fi aikata laifukan saboda raunin da ke tattare da bangaren ‘yan adawan.

Rahoton har ila yau ya nuna takaici kan laifukan da aka aikata, musamman ma a fannin fyade, inda aka gano cewa an samu rahotannin fyade 1,300 a jiha daya kacal, tsakanin watan Aprilu da Satumba a shekarar 2015.

Majiyoyi kwarara sun bayyana cewa kungiyoyin da ke marawa gwamnati baya, sun aikata fyade akan mata da dama, sannan suma kungiyoyi da ke marawa ‘yan tawaye baya da kuma zauna gari banza, suma sun aikata laifukan fyaden.

Kwamishinan kare hakkin bil’adama a ofishin Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra’ad Al Hussein, ya ce wannan yanayi da Sudan ta Kudu ta tsinci kanta a ciki, na daya daga cikin manyan matsaloli da ake fuskanta a duniya.

XS
SM
MD
LG