Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Birtaniya Ta Amince Da Fadada Filin Jirgin Sama Na Heathrow


Filin jirgin sama na Heathrow dake London

Majalisar wakilai da ta dattawa sun amince da gina hanyar saukan jiragen sama ta uku a filin jiragen Heathrow na birnin London a kasar Birtaniya

Bai daya Majalisar wakilan kasar Britaniya tayi na’am da shirye shiryen fadada filin sauka jiragen sama na Heathrow, filin saukar jiragen sama mafi girma a turai bayan an yi shekara da shekaru an yin muhawara akan irin tasirin da daukan wannan mataki zai yi.

Jiya Litinin Majalisar da ake cewa House of Commons ta jefa kuri’a dari hudu da goma sha biyar na amincewa gina hanyar saukar jiragen sama ta uku a Heathrow.

Gwamnatin Prime Minista Theresa May ta masu ra’ayin rikau da kungiyoyin yan kasuwa sun goyi bayan daukan wannan mataki sosai..

Gwamnati ta lashi takobin cewa zata fadada filin saukar jiragen sama ba tare da an taba aljihun yan kasar ba, ma’ana ba tare da an taba harajin da mutane suke biya ba, kuma matakin zai samar da aiyukan yi dubu dari.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
XS
SM
MD
LG