Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadda Aka Kai Ma Harin Guba A Birtaniya Tana Murmurewa


Firayim Ministar Birtaniya Theresa May

‘Yar tsohon dan leken asirin Rasha da aka cutar da sinadaran guba a wani harin da aka kai mata a Birtaniya, tace tana samun sauki cikin gaggawa.


Yulia ta fada a cikin wata sanarwar da yan sandan Birtaniya suka fitar a jiya Alhmis cewa, ta mike a makon da ya gabata kuma tana farin cikin kara samun kwarin jikinta.


Mahaifinta Sergei Skripal mai shekaru 66 a duniya, har yanzu yana cikin mawuyacin hali a wani asibitin Birtaniya biyo bayan hari da guba da akai musu ranar hudu ga watan Maris, lamarin da Birtaniya ke zargin Rasha da aikatawa. Harin gubar da aka kaiwa Skripal da ‘yarsa ya tado da tankiyar diplomaisya tsakanin kasashen yammacin duniya da Moscow, shigen zaman doya da manja na wajajen shekarun , 1950.


Birtaniya da Amurka da kawayensu na NATO sun kori jami’an diplomasiyar Rasha sama da 150 don nuna hadin kai da yin tir da harin gubar. Rasha dai tayi tsayin daka wurin musunta kai wannan harin, kana itama ta kori jami’an diplomaisyar kasashen yammacin duniyar dake cikin kasarta


A jiya Alhamis, an ga motocin bos bos guda uku da ake kyautata zaton suna dauke da jami’an diplomasiyar Amurka daga ofishin jakdancin Amurka a Moscow, bayan da wasu motocin dakon kaya sun kwashi kayayyakin su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG