Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Zartarwar Najeriya Ta Gabatar Da Gyare-Gyare Kan Kasafin Kudi Na Shekarar 2022


Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna
Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna

Majalisar zartaswar tarayyar Najeriya ta amince da shirin gyara kasafin kudin shekarar 2022 biyo bayan gyare-gyaren farko da majalisar dokokin kasar ta yi kan kudirin kasafin kudin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a shekarar 2021.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na Najeriya, Zainab Ahmed ce ta bayana hakan biyo bayan taron na su da suka saba gudanarwa a duk ranar Laraba a birnin tarayya, Abuja.

Ministar kudin ta ce sauye-sauyen da aka amince da a mikawa majalisar dokokin kasar za su bukaci a soke sashi na 10 da 11 da suka shafi hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC da kuma ayyukan hukumar leken asiri ta Najeriya a cikin kasafin kudin shekarar 2022 tare da maido da abin da ‘yan majalisar suka cire wanda ya kai Naira biliyan 103.

Ministar kudi ta kara da cewa sashi na 10 na magana ne kan wani tanadi da aka yi wanda zai baiwa hukumomin EFCC da NFIU damar karbar kaso 10 cikin 100 na duk wani tarin kudadde da kadarorin da suka sami nasarar kwato ko maidawa gwamnatin kasar.

Zainab ta ce suna neman a soke hakan ne saboda hakan ya sabawa dokokin wadannan hukumomi guda biyu kuma hakan ya saba wa dokar da ta shafi kasafin kudi da kuma dokar kudi ta shekarar 2021.

A wani bangaren kuma, sashi na 11 wani tanadi ne da aka yi wanda ya ce a yanzu haka ya ba wa ofisoshin jakadancin Najeriya da ma’aikatun kasar a waje izinin wannan dokar kasafi don kashe kudaden da aka ware musu karkashin sashin Capital Components a turance ba tare da neman amincewar ma’aikatar harkokin wajen kasar ba.

Kazalika, Zainab ta ce majalisar FEC ta kuma amince da wani kayyade huldar diflomasiyya tsakanin Najeriya da kasar Afirka ta Kudu la’akari da yarjejeniyar kasuwanci mara shinge nanahiyar Afirka.

XS
SM
MD
LG