Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Zartaswa Ta Haramtawa Likitocin Gwamnati Aiki A Asibitocin Kudi


A dai dai lokacin da uwargidan shugaban kasar Najeriya A’isha Buhari, ta koka da nuna damuwar ta kan halin ko-in-kula da kuma rashin samar da ingantacciyar hanyar kiwon lafiya a sibitin kasa dake fadar gwamanti a birnin Abuja.

Majalisar zartaswa ta Najeriya, ta dauki wani sabon mataki na haramtawa likitocin gwamnati yin aiki a wasu asibitoci masu zaman kansu, inda ake zargin cewa ana aikata almundahana dake cutar da tsare-tsaren kiwon lafiya musamman wadanda suka shafi talakawan kasa.

Dr Abu Yazid, kwararren likita ne kuma mai sharhi akan harkokin kiwon lafiya, ya bayyana cewa asibitoci sun lalace saboda rashin shugabanci na gari, domin a cewar sa, lokacin gwamnatin data gabata an bada kwangilolin bogi da dama, wasu an kammala yayin da wasu kuma an fidda kudadenne kawai.

Ya kara da cewa wannan na daga cikin dalilan da suka sa wasu likitoci da dama suka tsinci kawunansu cikin mawuyacin hali na rashin kayan aiki, dan haka ya kamata gwamnati mai ci yanzu ta samar da kayayyakin aikin da suka kamata.

Daga karshe Dr Yazid, ya bayyana cewa idan bera da sata, to daddawa ma nada wari, domin laifn ya rataya a dukkan bangarorin biyu, gwamnati bata biyan likitocin isassun kudin da zasu iya daukar dawainiyar kawunan su, dan haka idan har gwamnati zata gyara albashi n likitocin a cewarsa wannan doka bata da aibu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG