Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Jami’a Na Shirin Shiga Yajin Aiki A Ghana


Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Ghana UTAG
Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Ghana UTAG

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ghana (ko UTAG) ta ce mambobinta na shirin shiga yajin aikin na sai baba ta gani a Litinin.

Shugaban kungiyar malaman jami’o’in Farfesa Solomon Nunoo, ya ce matakin yajin aikin ya biyo bayan taron kasa da aka gudanar a ranar Juma’a. Matakin na nufin tursasa gwamnati ta inganta rayuwar malaman.

Malaman jami’o’in sun ce gwamnati ta gaza biyan bukatunsu duk da alkawuran da ta sha a tattaunawar cikin shekaru uku da suka gabata.

Sai dai magoya bayan gwamnati na nuna shakku kan lokacin da za a fara yajin aikin.

Sun ce gwamnatin na kokarin farfado da tattalin arzikin da annobar Covid-19 ta hallaka, wanda a cewarsu zai baiwa gwamnati damar biyan bukatun malaman jami’o’in.

Magoya bayan sun ce yajin aikin bata da tushe tun da ya dagula yunkurin gwamnatin kasar na magance kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Shugaban UTAG Farfesa Solomon Nunoo ya shaida wa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey cewa malaman jami’o’in ba za su koma ajujuwa sai sa’ar da gwamnati ta biya musu bukatunsu.

XS
SM
MD
LG